Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa

Babbar Jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zaben kasar INEC ke ci gaba da aikin sanarwa a yau Litinin.

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar
Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar REUTERS/Tife Owolabi
Talla

A wani taron manema labarai da PDP ta kira, shugaban jam'iyyar na kasa Uche Secondus ya ce hukumar ta INEC na fifita jam'iyya mai mulki ne a sakamakon.

Cikin kalamansa Mr Secondus ya ce sakamakon da INEC ke sanarwa babu gaskiya a cikinsa, face sinkin murda-murda da magudi.

Yanzu haka dai hukumar zaben Najeriyar ta sanar da sakamakon jihohi 5 ne na Najeriyar inda Jam'iyya mai mulki ke da rinjayen kuri'u.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.