Isa ga babban shafi
Sudan

Al-Bashir ya yi nadin sabbin mukamai bayan kafa dokar ta baci

Shugaban Sudan Omar Al-Bashir ya zabi sabon mataimaki da kuma Fira Minista, bayan bayyana kafa dokar ta baci a kasar da yayi a ranar Juma’a, wadda za ta shafe shekara guda tana aiki.

Shugaban Sudan Omar al-Bashir.
Shugaban Sudan Omar al-Bashir. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Yayin bayyana nadin sabbin mukaman, Shugaba al-Bashir ya maye gurbin tsohon mataimakinsa Bakri Hassan Saleh da ministan tsaron kasar Janar Awad Ibnoufas, yayin da ya bayyana Muhammad Tahir Ayala a matsayin sabon Fira Ministan kasar ta Sudan, wanda a baya shi ne tsohon gwamnan jihar Gezira.

Yayin gabatar da jawabi ta kafar Talabijin, Shugaba Al-Bashir yayiwa al’ummar Sudan alkawarin kafa tawagar kwararru da za su tsara hanyoyin fitar kasar daga cikin kangi na matsin tattalin arzikin da take fuskanta.

Tun a shekarar 2011, Sudan ta soma fuskantar karancin samun kudaden kasashen ketare musamman dala, bayan da Sudan ta Kudu, ta samu ‘yancin kai daga kasar, wadda ta balle tare da mafi akasarin arzikin rijyoyin danyen man da a baya suka mallaka tare da kasar ta Sudan.

Ranar 19 ga watan Disambar 2018, zanga-zanga ta barke a wasu biranen Sudan, bayan da gwamnati ta kara farashin Biredi, sai dai daga bisani zanga-zangar ta juye zuwa neman tilasta shugaba al-Bashir yin murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.