Kasashen Saharar Afrika 28 sun haramta auren jinsi - bincike
Wani Bincike ya nuna cewar sama da rabi na kasashen Afirka da ke Yamma da Sahara na amfani da dokar haramta auran jinsi, yayin da sauran suka samar da yanayin dokokin da ke kare irin wadanan mutane.
Wallafawa ranar:
Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta ce kasashe 28 daga cikin 49 na da dokokin da ke hukunta masu irin wannan dabi’ar da ta shafi auran jinsi.
Neela Ghoshal, jami’ar kungiyar ta ce kasashe irin su Mauritania da Sudan da Arewacin Najeriya na amfani da hukuncin kisa kan irin wadanan mutane, duk da ya ke babu wani da aka bayyana cewar an aiwatar masa da hukuncin.
Sai dai kasashe irin su Angola da Mozambique da Seychelles sun yi watsi da irin wadannan dokoki, yayin da Chadi da Uganda suka gabatar da sabbin dokoki masu tsauri akan irin wadannan mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu