Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Kotu ta daure jagoran 'yan adawar Zimbabwe

Kotu a Zimbabwe ta yanke wa wani madugun ‘yan adawa, Tendai Biti hukuncin biyan tara bisa samunsa da laifin bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana a watan Yuli na bara, inda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Tsohon ministan kudin Zimbabwe kuma jagoran babbar jami'iyyar adawa ta MDC Tendai Biti, yayin fita daga harabar kotu bayan yanke masa hukunci, a birnin Harare. 18/02/2019.
Tsohon ministan kudin Zimbabwe kuma jagoran babbar jami'iyyar adawa ta MDC Tendai Biti, yayin fita daga harabar kotu bayan yanke masa hukunci, a birnin Harare. 18/02/2019. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Biti, tsohon ministan kudin Zimbabwe, ya ayyana jam’iyyarsa ta MDC a matsayin wadda tayi nasara a zaben shugabancin kasar na ranar 30 ga watanYulin bara, lamarin da ya janyo zanga zangar kin jinin gwamnati, da ta yi sanadin mutuwar mutane 6 kafin sojoji su kwantar da tarzomar da kyar.

Alkalin kotun Gloria Takunda, ta umarci Biti ya biya dala 200, wato kudin tankin fetur daya, ko kuma ya shafe mako daya a gidan yari, zalika an kara da yankewa jagoran ‘yan adawar hukuncin daurin watanni 6.

Shugaban jam’iyyar adawar ta MDC, Nelson Chimasa wadda ya halarci zaman kotun ya ce hukuncin ya yayi illa ga dimokaradiyyar Zimbabwe.

Zimbabwe ta fada cikin rikici da tashin hankali biyo bayan zaben, wadda shi ne na farko da tsohon shugaba Robert Mugabe bai yi takara ba, dalilin murabus da yayi sakamakon karbe mulkin kasar da sojoji suka yin na dan lokaci a watan Nuwamban 2017.

Kasashen duniya dai sun bukaci shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya tabbatar da babu abin da zai taba lafiyar Tendai Biti, wadda ya taba rike mukamin ministan kudi daga shekarar 2009 zuwa 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.