Isa ga babban shafi
Kamaru-Boko Haram

Mayakan Boko Haram 187 sun ajje makamai a Kamaru

Akalla mayakan Boko Haram 187 ne suka koma kasar Kamaru daga Najeriya tare da mika kan su ga hukumomi bayan da suka janye daga yaki karkashin kungiyar wadda ke da karfi a arewa maso gabashin Najeriya.

Tubabbun Mayakan Boko Haram
Tubabbun Mayakan Boko Haram REUTERS/Ahmed Kingimi
Talla

Gwamnan yankin arewa mai nisa a kasar ta Kamaru Mijinyawa Bakari ya ce mayakan su 187 wadanda wasunsu ma sun shigo kasar ta Kamaru a kafa ne sun mika kan su ga mahukuntan garuruwan Kolofata da Meme.

A cewar Gwamna Mijinyawa Bakari bayan da mayakan suka mika kansu ga hukumomi, yanzu haka ana shirye-shiryen sanya su cikin wani shirin ba su horo na musamman don mayar da su cikin al'umma.

Yanzu haka dai tarin mayakan na shalkwatar rundunar hadin gwiwar kasashe masu yaki da Boko Haram da ta kunshi Sojin Najeriya Nijar Kamru da kuma Chadi.

Kawo yanzu dai akwai daruruwan tubabbun mayakan Boko Haram da ke karbar horon komawa cikin al'umma a kasar ta Kamaru inda bayan sun kammala horon gwamnati ta alkwarta basu filaye don rungumar sana'ar noma.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.