Isa ga babban shafi
Afrika-Bill gate

Za a iya samun kulawar lafiya a matalautan kasashen Afrika - Bill Gate

Attajirin kasar Amurka kuma shugaban kamfanin Microsofts, Bill Gates ya bayyana cewar ana iya samun kula da lafiya mai inganci a kasashen da suka fi ko wadanne talauci a Afirka muddin aka mayar da hankali akan magance cututtuka. Gates ya bayyana haka ne wajen taron shugabannin Afirka da aka yi a birnin Addis Ababa.

Gidauniyar Gates wadda ta kashe akalla Dala biliyan 15 a Afirka daga shekara ta 2000, a karshen mako ta kaddamar da wani shirin zuba jari mussaman ga gwamnatocin Afirka wajen kula da lafiya
Gidauniyar Gates wadda ta kashe akalla Dala biliyan 15 a Afirka daga shekara ta 2000, a karshen mako ta kaddamar da wani shirin zuba jari mussaman ga gwamnatocin Afirka wajen kula da lafiya Reuters
Talla

Attajirin na duniya Bill Gates wanda ya dade ya na bada tallafi domin kula da lafiyar al’umma, ya shaidawa shugabannin Afirka cewar, abin farin ciki shi ne da 'yan kudade kadan ana iya kula da lafiyar jama’a muddin aka mayar da hankali akai.

Gates ya ce ba dole ne sai kasa ta samu makudan kudade ba kafin ta mayar da hankali wajen kula da lafiyar jama’ar ta.

Shugaban na kamfanin Microsoft ya bayyana cewar samar da allurai da inganta hanyoyin haihuwa ga mata da kuma samar da magungunan da ke yaki da cututtuka na ‘antibiotics’ na taimakawa gaya wajen samar da lafiyar jama’a.

Gidauniyar Gates wadda ta kashe akalla Dala biliyan 15 a Afirka daga shekara ta 2000, a karshen mako ta kaddamar da wani shirin zuba jari mussaman ga gwamnatocin Afirka wajen kula da lafiya.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka mai barin gado, Paul Kagame na Rwanda, ya bukaci kowacce kasa da ta zuba akalla kashe 15 na kasafin kudin ta wajen kula da lafiyar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.