Sai dai kuma a karkashin saki kotun ta gindaya wa Gbagbo sharudda kuma zai kasance a Belgium har sai bayan daukaka kara da ake jin masu gabatar da kara za su daukaka.
Cikin sharuddan aka giundaya masa akwai na bukatar ya kai kansa kotun idan an neme shi, kuma zai ajiye passpo dinsa.
Ya kasance na farko tsohon shugaban wata kasa dakotun ta garkame shi tun shekara ta 2011, bayan da ya yi kememe ya ki sauka daga mulki bayan ya fadi zabe, har sai da aka zubar da jinni a kasar.