Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

'Yan tawayen Afrika ta tsakiya sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya

Wakilan Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tare da wakilan kungiyoyin 'yan Tawaye 14 sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, wanda shi ne irin sa na 8 da aka yi tun bayan kasar ta fada cikin tashin hankali a shekarar 2012.

Wani bangare daga cikin kungiyoyin 'yan tawayen da ke fada juna a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya bayan barkewar rikicin kasar a 2012
Wani bangare daga cikin kungiyoyin 'yan tawayen da ke fada juna a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya bayan barkewar rikicin kasar a 2012 AFP/ALEXIS HUGUET
Talla

Kungiyoyi 14 da ke dauke da makamai na rike da yankuna daban daban da ya kai kashi 80 na fadin kasar, tun bayan tashin hankalin da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi wa shugaba Francois Bozize a shekarar 2013, wanda ya jefa kasar cikin yaki.

Dakarun sojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da na Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin samar da zaman lafiya da ake kira MINUSCA da ke da sojoji 11,650 da 'yan Sanda 2,080 ke taimakawa wajen kare fararen hula daga hare hare.

Tun a shekarar 2013 aka ruguza kungiyar Seleka ta Musulman kasar wadda ta kifar da gwamnatin Bozize kana kuma ta ke fafatawa da kungiyar balaka ta kiristoci, abinda ya dada zafafa rikicin kasar.

Ana saran wannan sabuwar yarjejeniya ta bude kofar aje makamai da kuma yi wa 'yan Tawayen afuwa domin samun dawamammen zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.