Isa ga babban shafi

Ghana ta nuna damuwa da matakin Amurka na hana ta Visa

Kasar Ghana ta bayyana takaicin ta da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na takaita bai wa 'yan kasar bizar zuwa Amurka saboda rashin hadin kan da ta ce take fuskanta.

A makon jiya ne Amurkan da dau matakin fara hana Ghana Visa
A makon jiya ne Amurkan da dau matakin fara hana Ghana Visa iafrica.com
Talla

Minister harkokin wajen kasar, Shirley Ayorkor Botchway ta ce babu gaskiya cewar Ghana ba ta bai wa Amurka hadin kai wajen mayar da wasu yan kasar gida saboda shiga Amurka ba tare da izini ba.

Ministan ta ce kamar yadda doka ta tanada ofishin Jakandancin ta a Amurka na tantance mutane saboda rashin amincerwa da yadda aka tasa keyar wasu zuwa Ghanan a baya inda aka sanya musu ankwa a hannu da kuma daure su a kujerar jirgi.

A makon jiya ne Amurkan ta dau matakin fara hana al'ummar ta Ghana Visa bayan da ta zargi gwamnatin kasar da kin amincewa da karbar tarin al'ummarta da Amurkan ta ce suna zaune ba bisa ka'ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.