Isa ga babban shafi
Najeriya

Jirgin sama dauke da mataimakin Shugaban Najeriya ya fadi

Jirgin sama dauke da mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya fadi jim kadan bayan tashin sa a garin Kabba dake Jihar Kogi.

Farfesa Yemi Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo citypeopleonline
Talla

Bayanan dake zuwa daga Jihar sun ce babu wanda ya rasu a hadarin tsakanin mataimakin shugaban kasar da jami’an tsaron sa dake cikin jirgin.

Mai Magana da sunan mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yace Farfesa Osinbajo ya cigaba da gudanar da harkokin sa a Jihar Kogi kamar yadda aka tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.