Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun daukaka kara ta nemi Onnoghen ya kare kansa

Babbar Kotun daukaka kara a Najeriya ta ba da umarnin cewar, kotun da'ar ma’aikata na iya gudanar da shari’ar da ake yi wa Alkalin Alkalan kasar Walter Onnoghen, saboda haka kotun tayi watsi da bukatar san a dakatar da shari’ar.

Tubabben Alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Walter Samuel Onnoghen
Tubabben Alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Walter Samuel Onnoghen guardian.ng
Talla

Onnoghen ya ruga kotun daukaka karar ne domin kalubalantar tuhumar da ake masa na kin bayyana kadarorin da ya mallaka da kuma boye wasu asusun ajiyar kudaden waje dauke da makudan kudade.

Wannan hukunci ya tabbatar da hurumin kotun da'ar ma’aikatan na cigaba da shari’ar da ake yi wa babban mai shari’ar da aka dakatar Walter Samuel Onnoghen.

Tuni dai matakin dakatar da Onnoghen ya raba kan al’ummar kasar, inda wasu ke suka cewar ba’a bi ka’ida ba, yayin da wasu ke cewa bai dace ya cigaba da zama a mukamin ba, a daidai lokacin da ake tuhumar sa a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.