Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Harin Boko Haram ya tilastawa mutane dubu 30 tserewa daga Rann

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane dubu 30 ne suka tsere daga garin Rann na jihar Borno a Tarayyar Najeriya cikin kwanaki 2 tare da tsallakawa makociyar kasar Kamaru don kaucewa hare-haren kungiyar Boko Haram.

A cewar Majalisar Dinkin Duniyar wannan shi ne adadi mafi yawa a dunkule da al'umma suka fice daga garin na Rann
A cewar Majalisar Dinkin Duniyar wannan shi ne adadi mafi yawa a dunkule da al'umma suka fice daga garin na Rann irinnews.org
Talla

Wasu bayanai daga Jami’an tsaron sa kai da al’ummar garin Rann a jihar Borno baya ga na Majalisar Dinkin Duniya na nuna cewa cikin ‘yan kwanakin nan akwai yawaitar mutanen da ke tsallaka iyakar Najeriyar da Kamaru don tsira da rayukansu daga hare-haren Boko Haram da ya addabi yankin.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya cikin bayanan da ta fitar a yau din nan, adadi mafi yawa da ya fice daga garin na Rann shi ne na Mutane fiye da dubu 30 da suka tsere cikin kwanaki 2.

Ana dai ganin karin firgicewar al’ummar yankin baya rasa nasaba da harin ranar 14 ga watan wanda mayakan boko Haram suka kai kan sansanin sojin Najeriya da ke garin.

Cikin jawabinsa a Geneva, Babar Baloch kakakin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce a baya-bayan nan adadin mutanen da rikicin boko haram ya tilastawa barin muhallansu a Borno ya haura dubu 80.

A bangare guda suma kungiyoyin agaji da ke gudanar da ayyukan jinkai a garin na Rann sun ce harin ranar 14 ga watan nan ya tilastawa fiye da mutane dubu 9 barin muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.