A cewar majalisar ta na neman sanin ko shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi amfani da tanadin kundin tsarin mulki wajen sauke Onnoghen tare da maye gurbinsa da mai shari’a Tanko Mohammed.
Ka zalika Majalisar ta nemi sanin ko Shugaban na da hurumin sauke alkalin alkalai ba tare da sahalewarta ba, duba da tanadin sashe na 292 na kundin tsarin mulkin Najeriyar.
Karkashin sashen na 292 wanda ya yi bayanin kan matakan da za a bi wajen iya sauke alkalin alkalan bai fayyace matakin saukewar na din-din-din ne ko na wucin gadi ba.
Cikin wata sanarwar Majalisar mai dauke da sa hannun Yusuph Olaniyoni babban hadimin shugaban Majalisar Bukola Saraki, ta ce har gobe Talata batun dakatar da alkalin alkalan Najeriyar shi ne Majalisar za ta ci gaba da tattaunawa akai.
Tubabben alkalin alkalan Najeriyar dai na fuskantar tuhume-tuhumen rashawa baya ga kin bayyana ainahin arzikin da ya mallaka.