Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

An gano manyan kaburbura sama da 50 a Jamhuriyar Congo

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana gano manyan kaburbura sama da 50 a yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kowane daya daga cikin manyan kaburburan 50 da aka gano, yana dauke da akalla mutane 10.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kowane daya daga cikin manyan kaburburan 50 da aka gano, yana dauke da akalla mutane 10. News24
Talla

Gano manyan kabururan na zuwa ne, bayan rikicin kabilancin da ya auku a yankin, inda akalla mutane 890 suka hallaka.

An dai gwabza kazamin rikicin ne, tsakanin kabilun Banunu da Batende, a tsakanin ranakun 13 zuwa 18 ga watan disambar bara, a kauyuka hudu da ke yankin Yumbi.

Daraktan hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar dinkin duniya, Abdoul Aziz Thioye, ya ce kowane daya daga cikin manyan kaburburan 50 da aka gano, yana dauke da akalla mutane 5 zuwa 10.

Majalisar dinkin duniya, ta ce sama da mutane dubu 16 sun tsere daga kauyukan yankin na Yumbi zuwa kasar Congo Brazzaville da ke makwabtaka da Jamhuriyar ta Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.