Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya kan zargin rashawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da Alkalin alkalan kasar Walter Samuel Onneghen daga bakin aiki don fuskantar tuhume-tuhumen da ake masa kan cin hanci da rashawa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin nadin Walter Samuel Onnoghen a matsayin mukaddashin alkalin alkalan kasar bayan karewar wa'adin Mahmud Muhammad.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin nadin Walter Samuel Onnoghen a matsayin mukaddashin alkalin alkalan kasar bayan karewar wa'adin Mahmud Muhammad. NAN
Talla

Cikin wani sakon Twitter da wani Jami’in shugaban kasar Bashir Ahmad ya wallafa ya ce Buhari ya umarci Mr Ibrahim Tanko Muhammad ya maye gurbin mai shari’a Onnoghen a matsayin mukaddashi kafin kammala shari’ar da ake masa kan rashawa.

Matakin na Buhari na zuwa kasa da wata guda da Najeriyar ke shirin gudanar da babban zabe da ya kunshi na Shugaban kasa da ‘yan majalisu na tarayya a ranar 16 ga watan Fabarairu.

Mai shari'a Onnoghen dai na fuskantar tuhume-tuhume masu alaka da gaza bayyana ainahin dukiyar da ya mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.