Isa ga babban shafi
Zimbabwe-Afrika ta kudu-Amurka

Jam'iyyar ANC ta bukaci janye takunkumai daga kan Zimbabwe

Jam’iyyar ANC mai mulkin Afrika ta Kudu, ta bukaci Amurka ta janye takunkuman karya tattalin arzkin da ta kakabawa makwabciyarsu Zimbabwe, kasar da a halin yanzu mutane 12 suka hallaka, yayin arrangama tsakanin, jamián tsaro da masu zanga-zanga kan karin farashin man Fetur.

Yanzu haka dai dubban al'umma na ci gaba da bore kan matsin rayuwar da su ke fuskanta a kasar ta Zimbabwe bayan karin farashin man fetur a baya-bayan nan.
Yanzu haka dai dubban al'umma na ci gaba da bore kan matsin rayuwar da su ke fuskanta a kasar ta Zimbabwe bayan karin farashin man fetur a baya-bayan nan. Jekesai NJIKIZANA / AFP
Talla

Yayin zantawa da manema labarai a birnin Johannesbourg, daya daga cikin ‘yan kwamitin zartarwa jamíyyar ta ANC, Lindiwe Zulu, ya ce a zatonsu, zaben watan Yulin bara da ya kawo karshen mulkin Robert Mugabe, zai sa kasashen da suka kakabawa kasar takunkumai su dage, la'akari da banbancin manufofin tattalin arziki, da na kasashen ketare tsakanin sabon shugaba Emmerson Mnangagwa, da kuma tsohon shugaba Mugabe.

A cewar Lindiwe Zulu duk da saukar Robert Mugabe daga shugabancin Zimbabwe a watan Nuwamban 2017, har yanzu kasar tana karkashin takunkumin karya tattalin arzikin da Amurka ta kakaba mata a zamanin mulkin Mugabe da ya shafe shekaru 37 bisa mulki kafin yin Murabus.

Zanga-zangar baya bayan nan da sabuwar gwamnatin Emmerson Mnangagwa ke fuskanta kan Karin farashin mai, na da alaka da matsin tattalin arzikin da ‘yan kasar ke fuskanta da rashin aikin yi da ya kai kashi 80 cikin dari, matsalar da kamarinta ya addabi kasar shekaru 10 baya, wanda kuma cikin wannan yanayi ne, Sabon shugaba Emmerson Mnangagwa ya karbi ragamar jagorancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.