Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 19/08 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 19/08 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/08 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 16/08 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 19/08 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/08 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Najeriya ta amince da Naira dubu 27 a matsayin mafi karancin albashi

media Kafin yanzu dai asha kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriyar da kungiyoyin kwadago musamman gwamnatocin jihohi wadanda suka kekasa kasa kan cewa baza su iya biyan adadin da kungiyoyin suka gindaya na dubu 30 ba. REUTERS/Afolabi Sotunde

Majalisar kolin Najeriya da ta kunshi shugaban kasa da tsaffin shugabannin kasa da Gwamnonin Jihohi da kuma babban alkalin kasa mai ci da wadanda suka yi ritaya ta amince da naira dubu 27 a matsayin albashi mafi karanci a Jihohi, yayin da ma’aikatan tarayya kuma za su karbi naira dubu 30.

Ministan kwadago Chris Ngige ya bayyana haka bayan zaman majalisar da ya gudana a fadar shugaban kasa, inda ya ce tuni aka mikawa Majalisar kasa kudirin domin amincewa da shi dan ganin an fara biyan ma’aikata.

Cikin wadanda suka halarci taron da ya gudana a karkashin shugaba Muhammadu Buhari, sun hada da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo da tsoffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Abdusalami Abubakar da Goodluck Jonathan da Ernest Shonekan.

Tsawon lokaci dai kungiyoyin kwadagon Najeriyar suka shafe suna tattauna daban-daban da gwamnatin kasar kan karin mafi karancin albashin, ko da dai jihohin a baya sun yi tayin naira dubu 22 amma kungiyoyin suka yi watsi da shi.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure