Isa ga babban shafi
Algeria

Algeria ta tsaida lokacin zaben shugabancin kasar

Gwamnatin Algeria ta bayyana 18 ga watan Afrilu mai zuwa, a matsayin ranar da zaben shugabancin kasar zai gudana.

Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika, mai shekaru 81 mai fama da rashin lafiyar mutuwar barin jiki.
Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika, mai shekaru 81 mai fama da rashin lafiyar mutuwar barin jiki. AFP/Eric FEFERBERG
Talla

Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko shugaba mai ci AbdelAziz Bouteflika zai sake tsayawa takara ba, la’akari da cewa manyan kusoshin gwamnatin kasar, sun bayyana goyon bayan ya sake neman wani wa’adin shugabanci.

Bouteflika mai shekaru 81, ya kasance bisa shugabancin kasar Algeria tun daga shekarar 1999, sai dai daga shekarar 2013, ya rage fita cikin jama’a sakamakon fama da cutar mutuwar barin jiki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.