Isa ga babban shafi
Sudan

Kungiyar Likitocin Sudan ta shiga yajin aiki da zanga-zanga

Kungiyar Likitoci a Sudan ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani dai dai lokacin da daruruwan masu zanga zanga su ka yi jerin gwano bayan halartar jana’izar mutanen da aka kashe jiya a birnin Khartoum na kasar ciki har da Likita guda. Masu zanga zangar sun kekashe kasa sai shugaba Omar Hassan Al Bashir y asauka daga kujerar sa.

Ana ganin tsundumar likitocin yajin aiki da kuma bara baya ga masu zanga-zangar baya rasa nasaba da kisan mambanta a jiya Alhamis da ake zargin jami'an tsaro da aikatawa.
Ana ganin tsundumar likitocin yajin aiki da kuma bara baya ga masu zanga-zangar baya rasa nasaba da kisan mambanta a jiya Alhamis da ake zargin jami'an tsaro da aikatawa. Photo: Mohamed Nureldin Abdallah/Reuters
Talla

Tarin masu zanga zangar sun ce ba za su daina ba, kuma ba sa jin tsoro, yayinda su ke tattaki a yankin Buri da ya yi kaurin suna wajen adawa da gwamnatin shugaba Omar Hassan al Bashir.

Faifan bidiyon da aka nada ya nuna maza da mata da suka rufe fuskokinsu, inda su ke sukar gwamnati suka kuma kira ga shugaban kasar ya sauka daga mukamin sa.

Kungiyar kwararru ta mutanen Sudan da ke jagorancin zanga zangar a fadin kasar ta ce mutane 3 aka kashe jiya alhamis sakamakon arangamr da akayi tsakanin su da Yan Sanda, cikinsu har da wani yaro da kuma likita.

Mai Magana da yawun kungiyar Mohammed al Asbat ya tabbatar da mutuwar mutum na uku.

Hukumomin Sudan basu tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba, sai dai sun bayyana cewar adadin mutanen da suka mutu gaba daya sun kai 24, yayin da kungiyar Amnesty International ta ce adadin ya zarce 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.