Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya nada sabon babban sufeton 'yan sandan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin Muhammad Adamu a matsayin sabon Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya domin maye gurbin Ibrahim Idris wanda ya kawo karshen wa’adin aikin sa yau.

Sabon babban sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammad Abubakar Adamu.
Sabon babban sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammad Abubakar Adamu. RFI
Talla

Sabon Sufeto Janar Muhammad Adamu ya fito ne daga Jihar Nasarawa, kuma kafin wannan nadin, malami ne a Cibiyar horar da manyan jami’ai ta NIPPS da ke Jihar Plateau a matsayin mataimakin Sufeto Janar.

Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tsohon Sufeto Janar Ibrahim Idris suka likawa sabon Sufeto Janar din sabon mukamin sa a fadar shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.