Isa ga babban shafi
Sudan

Zanga-zanga ba za ta ture ni daga mulki ba- Al-Bashir

Shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir ya ce zanga-zangar da wasu ‘yan kasar ke yi don tilasta masa yin Murabus ba za ta yi tasirin wajen sauya gwamnatinsa ba.Al-Bashir ya bayyana hakan ne a yankin Darfur, lokacin da ya ke jawabi ga taron magoya bayansa a babban birnin yankin Niyala, yankin da ko a ranar lahadi sai da ‘yan sanda suka tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga.

Shugaban kasar Sudan Omar Al Bashir.
Shugaban kasar Sudan Omar Al Bashir. ASHRAF SHAZLY | AFP
Talla

A cewar shugaban na Sudan, hanya daya ta sauya gwamnati shi ne kada kuri’a, kuma a shekarar 2020, ‘yan kasar Sudan za su tantance waye gwaninsu, a zaben shugabancin kasar da Al-Bashir ya sha alwashin sake neman wa’adi na gaba.

Ranar 19 ga Disamba zanga-zanga ta soma kan adawa da karin farashin Biredi a biranen kasar ta Sudan, wadda ta juye zuwa ta kyamar gwamnati inda suka rika kururuwar neman tilasta saukar shugaba al-Bashir daga mulki.

Kwamitin da Sudan ta kafa don sa ido kan boren da wasu ‘yan kasar ke yi, ya ce mutane 24 sun mutu bayan soma zanga-zangar daga Disamba zuwa yanzu.

Sai dai kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce yawan wadanda suka rasa rayukansu ya kai akalla 40, a dalilin arrangamar masu zanga-zangar da jami’an tsaro a lokuta daban daban.

Shugaba al-Bashir da kotun duniya ta ICC ke nema ‘ruwa a jallo’ ya dora alhakin tashe tashen hankulan kan wasu makiyan Sudan a ciki da wajen kasar, inda kuma ya zargi Amurka da jefa kasar cikin kangin wahala, bayan kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki a shekarar 1997 zuwa 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.