Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Mutane 11 suka mutu sakamakon tarzoma a Congo

Rahotanni daga Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 11 sakamakon tarzomar da aka yi bayan da hukumar zabe ta bayyana Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugabancin kasar.Mafi yawan mutanen sun mutu ne a garin Kikwit da ke lardin Kwilu, wanda shi ne babbar cibiyar magoya bayan Martin Fayulu da ke ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben amma kuma ake neman kwace masa wannan nasara.

Félix Tshisekedi dan takara da ya lashe zaben DR Congo
Félix Tshisekedi dan takara da ya lashe zaben DR Congo REUTERS/Baz Ratner
Talla

Hukumar zaben Dimokuradiyyar Congo ta bayyana dan takarar adawa Felix Tshisekedi, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka yi ranar 30 ga watan disambar sa ya gabata.

Wannan ne dai karon farko a tarihi, da dan takarar adawa ya yi nasarar kayar da dan takarar jam’iyya mai mulki a kasar, to sai dai tuni Martin Fayulu da wasu kasashe suka, yi zargin cewa an tafka magudi.

Abvdoulaye Issa ya duba mana labarin a wannan rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.