Kar ku sake zabar gwamnan da ya gaza biyan hakkin ma'aikata- Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya su guji sake zaben duk wani gwamna da ya gaza biyan hakkokin ma’aikata a tsawon lokacin da ya dauka ya na shugabanci duk da kudaden da jihohin ke samu daga gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
Muhammadu Buhari wanda ke neman kujerar shugabancin Najeriyar a zagaye na biyu karkashin Jam’iyyar APC ya ce yana takaicin yadda gwamnoni ke iya barci cikin nutsuwa alhalin sun gaza biyan albashin ma’aikata.
A zantawarsa da wata kafar yada labaran Amurka, Muhammadu Buhari ya ce rashin adalci ne gwamnonin su juyar da hakkokin ma’aikata don wasu abubuwa na kashin kansu bayan karbar kudade daga hannun gwamnatin kasar.
Ba tun yanzu ba dai shugaban Najeriyar ke kokawa da yadda gwamnatocin jihohin kasar ke gaza sauke nauyin ma'aikata ciki har da wadanda suka yi ritaya tsawon lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu