Farfesa Khalifa Dikwa kan yadda Buhari ya amince cewa an fuskanci koma baya a yaki da Boko Haram
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:13
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince cewa ana samun koma-baya a fafutukar kakkabe mayakan Boko Haram musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.A yayin wata hirarsa da aka watsa ta kafar talabijin ta Arise a cikin daren da ya gabata, shugaba Buhari ya amince cewa, sojojin kasar na fuskantar matsin lamba daga mayakan na Boko Haram da ke amfani da salon yakin sunkuru. Shugaban ya kuma amince cewa, sojojin kasar na fama da matsalar rashin karfafa musu guiwa a fagen-daga, amma ya ce, suna kan kokarin shawo kan wannan matsalar. Hakan muka tuntubi Farfesa Khalifa Dikwa ga kuma abin da ya ke cewa.