Isa ga babban shafi
Najeriya-NLC

Zanga-Zanga za mu fara ba yajin aiki ba - NLC

Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta ce za ta tsunduma zanga-zanga a gobe Talata kan yadda gwamnatin kasar ta gaza cimma matsaya kan mafi karancin albashin ma’aikata amma hakan baya nufin umartar daukacin ma'aikatan kasar su tafi yajin aiki.

A cewar NLC Ilahirin mambobinta za su fito a goben don fara zanga-zangar wadda ke matsayin mataki na gaba da za su dauka don tirsasa gwamnati amincewa da matakin kara albashin ma'aikatan zuwa Naira dubu 30.
A cewar NLC Ilahirin mambobinta za su fito a goben don fara zanga-zangar wadda ke matsayin mataki na gaba da za su dauka don tirsasa gwamnati amincewa da matakin kara albashin ma'aikatan zuwa Naira dubu 30.
Talla

Babban sakataren NLC Dr Peter Ozo-Eson ya tabbatarwa kamfanin dillacin labaran kasar cewa matakin da za su fara dauka daga goben ba wai yajin aiki ba ne kamar yadda suka yi a baya, yana mai cewa zanga-zanga ce da za ta gudana a ilahirin sassan kasar.

Kungiyar kwadagon ta NLC dai ta tsaya kan bakanta wajen ganin lallai gwamnatocin kasar sun amince da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata sabanin Naira dubu 18 da su ke karba a halin yanzu.

Tun a ranar 17 ga watan Disamban bara, NLC ta sha alwashin maukar Fadar shugaban kasa ta gaza mika kudirin Karin albashin gaban majalisar don zamowa doka kafin 31 ga watan, babu shakka za ta dauki mataki na kashin kanta.

Yanzu haka dai Gwamnatocin jihohin kasar sun tsaya sun amince da kara mafi karancin albashin ma'aikatan zuwa Naira dubu 22 matakin da kungiyoyin kwadagon Najeriyar suka yi watsi da shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.