Isa ga babban shafi
Gabon

Sojoji na gab da juyin mulki a Gabon

Yanzu haka ana can ana jin karar harbe-harben bindiga a birnin Libreville na kasar Gabon, bayan da wasu sojoji suka fito a gidan rediyon mallakin gwamnati tare da karanta sanarwar da ke cewa, za su kafa wata majalisar koli domin dawo da martabar kasar.

Gidan Rediyo da na Talabijin na gwamnati da sojojin suka sanar da juyin matsayarsu ta kafa majalisar koli
Gidan Rediyo da na Talabijin na gwamnati da sojojin suka sanar da juyin matsayarsu ta kafa majalisar koli afp
Talla

Da misalin karfe 4 na safe agogon kasar ne sojojin suka karanta wannan sanarwa wadda ta yi watsi da jawabin da shugaban kasar mai jinya a kasar Morocco ya gabatar,, yayin da wasu rahotanni ke cewa an fara ganin wasu sojoji na jan daga a zagayen muhimman gine-ginen gwamnati.

Sanarwar wadda lafanar Ondo Obiang Kelly, karafin hafsa na rundunar da ake kira Repubican Guard ya karanta ta ce, za su sanar da kafa wata majalisar koli domin kare martabar kasar.

Har ila yau sanarwar sojojin ta bukaci illahirin manyan jami’an gwamnati, da na hukumomin kasar da ma shugabannin kungiyoyin kwadago da na fararen hula domin su bayyana a majalisar dokokin kasar a yau Litinin.

Sojojin sun kuma bukaci takwarorinsu da su kama illahirin muhimman fannoni sufuri, da rumbunan ajiye makamai da filayen jiragen sama da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.