Sudan: 'Yan adawa sun bukaci El-bashir ya sauka daga mulki
‘Yan adawa a Sudan sun bukaci shugaban kasar Umar Al-bashir da ya gaggauta sauka daga karagar mulki, bayan share sama da makonni biyu ana tarzomar nuna kin jinin mulkinsa.
Wallafawa ranar:
Ko a jiya juma’a sai dai ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa jama’a da suka bukaci gudanar da zanga-zanga bayan kammala sallar juma’a.
A ranar 19 ga watan disambar da ya gabata ne aka fara zanga-zanga a kasar, bayan da gwamntin ta yanke shawarar kara kudin biredi, to sai dai mafi yawan masu tarzomar na neman samun karin ‘yanci ne a kasar da shugaba El-bashir ke mulki sama da shekaru 30.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu