Isa ga babban shafi
Masar

Dakarun Masar da na Isra'ila sun hada gwiwa a Sinai - el Sisi

Shugaban Masar Abdul Fattah el-Sisi, ya ce gwamnatinsa na aiki tare da Isra’ila wajen yakar kungiyoyin ‘yan tada kayar baya da ke yankin Sinai.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi.
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugaban na Masar, ya bayyana haka ne cikin wata ganawa da ya yi da kafar yada labarai ta CBS, wadda rahotanni suka ce daga baya, gwamnatin ta Masar ta nemi da kada a watsa hirar.

Ko da yake gwamnatin ta Masar ba ta bayyana dalilanta na neman dakatar da watsa hirar ba, wata majiya ta ce, babban dalilin shi ne fargabar abinda ka biyo baya a ciki da wajen kasar, kan batun hadin gwiwa tsakanin sojojin na Masar da kuma na Isra'ila wajen yaki a yankin Sinai.

Sai dai kafar yada labaran ta CBS ta sanar da kin amincewa da bukatar ta gwamnatin Masar, inda kuma ta tsayar da Lahadin nan a matsayin ranar da za ta watsa cikakkiyar tattaunawar da ta yi da shugaban na Masar mai tsawon sa’a guda.

Ko a shekarar bara, rundunar sojin Masar ta musanta rahotannin cewa ta hada giwa da sojin Isra’ila wajen yakar kananan kungiyoyin da ke biyayya ga mayakan ISIS a arewacin yankin Sinai da ke kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.