Isa ga babban shafi
Najeriya-NLC-TUC

Najeriya ta gana da NLC da TUC kafin zanga-zangarsu a makon gobe

Gwamnatin Najeriya ta dawo tattaunawa da shugabannin kungiyoyin kwadago na kasar dangane da batun fara amfani da sabon mafi karancin albashin ma’aikata don dakile zanga-zangar da kungiyoyin suka shirya gudanarwa a ranar 8 ga watan Janairu.

A ranar 8 ga wata ne hadakar kungiyoyin da suka kunshi na TUC da NLC da kuma kananan kungiyoyi suka shirya fara wata zanga-zangar adawa da yadda gwamnatin ta gaza cimma matsaya kan batun mafi karancin albashin.
A ranar 8 ga wata ne hadakar kungiyoyin da suka kunshi na TUC da NLC da kuma kananan kungiyoyi suka shirya fara wata zanga-zangar adawa da yadda gwamnatin ta gaza cimma matsaya kan batun mafi karancin albashin. rfi hausa
Talla

Taron wanda yanzu haka ke gudana a Abuja babban birnin kasar mahalartansa sun hada da shugaban kungiyar kwadago ta NLC da TUC da ministar kudi Zainab Ahmed da ministan kasafi da tsare-tsare Udoma Udo Udoma da kuma Ministan kwadagon Najeriyar Chris Ngige.

Kungiyoyin kwadagon dai har yanzu suna kan bakarsu ta ganin gwamnati ta biya Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar sabanin Naira dubu 18 da su ke karba a halin yanzu.

Tuni dai gwamnatocin jihohin Najeriyar suka shata layin cewa baza su iya biyan Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi ba, ko da dai shugaban kasar a wancan karon ya amince da kafa wani kwamiti don bibiyar bukatar.

A bangare guda itama kungiyar kwadago ta tsaya kan cewa baza ta cimma wata yarjejeniya da gwamnatin Tarayya ba face idan ta mika kudirin biyan mafi karancin albashin gaban majalisun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.