Isa ga babban shafi
Nijar

Dosso ta lashe takobin kokuwar 2018

Jihar Dosso ta kafa tarihi a gasar Kokuwar galgajiya da aka kamala a jihar Tillabery. Bayan zamani su Salma Dan Rani, Kadri Abdou da aka fi sani da sunan Issaka-Issaka ya lashe takobi bayan da ya kayar da Nura Hassan wani dan kokuwar jihar Dosso bayan mituna 4 da dakikoki 14.

Kadri Abdou dan kokuwar Dosso
Kadri Abdou dan kokuwar Dosso ONEP -Niger
Talla

Kayin na baiwa sabon sarki Kadri Abdou da aka sani da sunan Issaka-Issaka damar lashe kyaututuka ko tukuici da suka hada da doki daya, takobi da kudi tsaba milyan 14 da 800 na kudin cfa.

Hukumar kokuwa ta kasa ta bayyana cewa gasar shekara ta 2019 zata gudana ne a watan Disemba a jihar Maradi.

Wannan dai ne karo na uku da Issaka-Issaka ke lashe takobin kokuwar Nijar.

A shekarar da ta gabata dan wasa na jihar Damagaram ko Zinder Tasiu Sani ne ya lashe takobin, yayinda a wannan karo bai samu sa’ar sake kasancewa a wannan matsayi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.