Damuwa dangane da makomar wasu baki a Algeria
Hukumar kula da ‘yan gundun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai damuwa matuka dangane da makomar wasu baki mafi yawansu ‘yan asalin kasashen larabawa da mahukuntan Algeria suka tsare a wani yankin da ke kudancin kasar.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen zai kai 120, da suka hada da yan Syria, Falesdinawa da kuma yan kasar Yemen, yanzu haka ana tsare da su ne a wani sansani da ke garin Tamarasset da ke iyakar kasar da jamhuriyar Nijar.
Da jiamawa ana zargin hukumomin Algeria da kaucewa batun kare hakokin bil Adam musaman baki yan cin rani dake tsallakawa daga kasar zuwa Turai.
Ya zuwa yanzu hukumomin Algeria basu ce upon dangane da wannan zargi daga hukumar kula da yan gudun hiijira.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu