Isa ga babban shafi
Afrika

Cocin Katolika a Congo ta ce ta san wanda ya lashe zaben kasar

Majalisar shugabannin cocin Katolika a jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, ta ce ta san wanda ya yi nasara a zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar lahadin da ta gabata yayin da hukumar zabe ke cewa abu ne mai yiyuwa a jinkirta fitar da sakamakon wannan zabe.

Dakon sakamakon zaben DRConco
Dakon sakamakon zaben DRConco REUTERS/Baz Ratner
Talla

Mai magana da yawun shugabannin cocin Donatien Nshole a jiya alhamis, ya bayyana cewa ‘yan kura-kuran da aka samu a lokacin zaben, ba za su iya canza sakamakon abin da jama’a ta zaba a ranar ta lahadi ba, saboda haka suna fatan za a fitar da sakamakon kamar yadda ya ke.

Wasu kasashen da suka hada da Faransa sun bukaci gwamnatin Jamhuriyar Congo ta mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, biyo bayan matakinta na katse hanyar sadawar Intanet da kuma takaita aikin wasu ‘yan jarida da ke sa ido kan zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar Lahdi.

Kiran dai na zuwa a dai dai lokacin da shugaban hukumar zaben Jamhuriyar ta Congon Corneille Nangaa, ya ce akwai yiwuwar dage lokacin bayyana sakamakon zaben daga ranar lahadi mai zuwa, zuwa wani lokaci daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.