Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Sa’idu Ahmad Dukawa kan takaddama game da wanda zai yi nasara a zaben Congo

Wallafawa ranar:

Yayin da ake dakon sakamakon zaben Jamhuriyar Congo, ‘yan adawa sun ce daya daga cikin ‘yan takararsu ne zai yi nasara, a dai dai lokacin da shi ma dan takara Emmanuel Ramazani na bangaren gwamnati ke ikirarin samun nasarar.Ikirarin ‘yan takarar dai ya zo ne yayin da wasu ke fargaba kan abinda zai biyo bayan fitar da sakamakon zaben. Dangane da halin da ake ciki a Jamhuriyar Congon, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Sa’idu Ahmad Dukawa, na sashin nazarin kimiyyar siyasa da ke jami’ar Bayero a Kano.

Yanzu haka dai bangarorin adawa na ci gaba da nuna cewa dan takararsu ne ya lashe zaben yayinda suma na bangaren jam'iyya mai ci ke ganin na su ne zai yi nasara a zaben mai cike da sarkakiya.
Yanzu haka dai bangarorin adawa na ci gaba da nuna cewa dan takararsu ne ya lashe zaben yayinda suma na bangaren jam'iyya mai ci ke ganin na su ne zai yi nasara a zaben mai cike da sarkakiya. REUTERS/Baz Ratner
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.