Burutai ya bukaci jajircewar sojin Najeriya a yaki da Boko Haram
Babban Hafson sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Yusuf Tukur Burutai ya bukaci dakarun sojin kasar su tashi tsaye a yakin da su ke da Boko haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Cikin sakonsa na Kirsimeti Burutai ya musanta zarge-zargen da ake na cewa har yaznu mayakan na Boko Haram su na da sauran karfi, inda ya ce a bayyana ta ke sojin Najeriya sun yi rawar gani wajen murkushesu.
A cewar Burutai cikin kalaman na sa da ke matsayin jan kunne ga Sojin na Najeriya, ka da su yarda bayanan karya da ake yadawa na kara yawan adadinsu da aka kashe a fagen daga ko kuma karfin da Boko Haram ke da shi ya rage musu karsashi, yana mai cewa kadan ya rage a ga bayan kungiyar.
Burutai ya dora laifin bayar da bayanan karya kan halin da ake ciki a yakin da Boko Haram kan masu farfagandar ganin sun rage karsashin dakarun.
Cikin jawaban na sa Janar Burutai ya yi fatan Dakarun su gudanar da bukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin lumana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu