Kamfanonin Eni da Shell na da masaniya wajen baiwa wasu Najeriya cin hanci
Wata mai shari’a a kasar Italiya ta bayyana cewar kamfanonin hakar man Eni da Shell na da masaniyar cewar an baiwa wasu yan siyasa da jami’an gwamnati Najeriya cin hanci wajen cinikin rijiyoyin mai a shekarar 2011 a kasar.
Wallafawa ranar:
Kamfanonin biyu sun sayi rijiyar mai lamba OPL 245 akan kudi sama da dala biliyan 1 da miliyan 300, yayin da yan siyasa da da wasu jami’an gwamnati suka yi rub da ciki da Dala biliyan guda da miliyan 100.
Mai shari’ar Giusy Barbara tace kamfanonin biyu na sane da wannan aika aika, abinda yasa aka daure mutane biyu da suka shiga tsakani wajen cinikin, Emeka Obi da Gianluca Di Nardo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu