Isa ga babban shafi
Afrika

Firaministan kasar Mali ya ziyarci arewacin kasar

Gwamnatin kasar Mali ta bayyana shirin kara yawan jami’an tsaro a birnin Timbuktu, sakamakon cigaba da tabarbarewar tsaro a yankin.

Soumeylou Boubeye Maïga  Firaministan kasar Mali
Soumeylou Boubeye Maïga Firaministan kasar Mali MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Firaministar kasar Soumeylou Boubeye Maiga ya bayyana haka, bayan ya ziyarci yankin, inda yake cewa za’a tura karin yan sanda da soji da Jandarmomi 350.

Soumylou Boubeye Maiga ya kuma ce gwamnatin zata kafa rundunar tsaron iyaka da kuma kara taimakawa jami’an tsaro da kayan aiki. A watan Oktoban shekarar bana dai ne Firaministan Mali Soumeylou Boubeye Maiga ya kai wata ziyara zuwa Tenenkou da Toguere Coumbe dake cikin yankin Mopti a tsakiyar kasar ta Mali, yankin dake fama da rashin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.