Isa ga babban shafi
Duniya

Samun nasara kan ‘Yan ta’adda ya dogara ga sauya tunaninsu -Masana

Wasu Masana tashe tashen hankula a Duniya dake da nasaba da akida sun bayyana cewar kasashen Yammacin duniya ba zasu iya magance matsalar da ake samu na tsatsauran ra’ayi ba muddin basu dauko gyara tun daga tushe ba.

Harin ta'addanci a Burkina Faso
Harin ta'addanci a Burkina Faso RFI / Yaya Boudani
Talla

Katherine Zimmerman, wadda ta rubutawa wata Cibiyar Amurka rahoto kan ‘Ayyukan ta’addanci, tsari da kuma yadda yake karuwa’, tace bayan samun nasarar murkushe masu tsatsauran ra’ayi a bayyane, nasarar na dakushewa domin samun masu rike da irin akidar su.

Zimmerman tace duk wani sojan da ya shiga wannan yaki da masu irin wannan ra’ayi, ya fahimci yadda matsalar take.

Jami’ar tace sojojin sun fahimci cewar, nasarar da suke samu takaitacciya ce, domin suna magance barazanar da ake gani ne kawai a fili, yayin da samun nasarar din-din-din ta dogara da sauya tunanin masu rike da irin wannan akidar.

Zimmerman tace mayakan IS da aka kora daga Syria da Iraqi sun koma inda suka fito, inda suke cigaba da dasawa mutane mummunar akidar su, wadda ke iya zama matsala nan gaba.

Jami’ar ta bayyana kasashen da ake fuskantar irin wannan matsalar da suka hada da Yemen da Syria da Iraqi da Afghanistan da Libya da Mali da Najeriya da kuma Somalia.

Zimmerman tayi gargadin cewar, kasashen Yammacin duniya na hanyar samun nasarar karawar da suke yi da yan ta’adda a filin yaki, amma kuma samun nasara akan su ya danganci sauya akidar da suke cusawa jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.