Sudan ta Kudu za ta baiwa jami'an lafiyarta rigakafin Ebola
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, tace hukumomin Sudan ta kudu za su yiwa jami’an kula da lafiyar su allurar rigakafin cutar Ebola saboda mu’amalar da suke yi kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Congo.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar lafiyar kasar tace rigakafin da za ta yi tare da hukumar lafiyar, zai mayar da hankali kan jami’an ta dake aiki a Juba, Yei, Yambio da kuma Nimule.
Kasar Sudan ta kudu na daga cikin kasashen dake iyaka da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo inda cutar ta hallaka mutane 271 ya zuwa yanzu.
A ranar 19 ga watan Disamba za’a soma aikin yiwa ma’aikatan lafiyar na Sudan ta Kudun rigakafi, kuma tuni aka ware maganin rigakafin na Ebola 2,160.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu