Bakonmu a Yau
Dr Mannir Bature mataimakin shugaban kungiyar likitoci a Zamfara kan bayanan da ke nuna mata masu ciki 30 na mutuwa kowacce rana
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:38
Kungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Zamfara ta ce akalla mata masu juna biyu 30 ne ke mutuwa a kowace rana cikin jihar, a dalilin matsaloli da suke fuskanta na lafiya.Mataimakin shugaban kungiyar likitocin jihar Dr Mannir Bature ne ya bayyana haka yayin ganawarsu da ‘yan takarar da ke neman kujerar gwamnatin jihar ta Zamfara. Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Mannir Bature mataimakin shugaban kungiyar likitocin ta jihar Zamfara kan kalubalen dake fuskantarsu da kuma mafita.