Isa ga babban shafi
Sahel-Ta'addanci

G5 Sahel na bukatar karin kudin yaki da ta'addanci

Kungiyar tarayyar Turai EU da Faransa sun ce adadin kudin da su ke bukata don tallafawa yankin sahel wajen yakar ayyukan ta’addanci ya karu zuwa euro biliyan 1 da miliyan dari 3, bayan tsanantar ayyukan ta’addanci da kuma ‘yan tada kayar baya a kasashen yankin na Sahel.

A cewar EU tsanantar ayyukan ta'addanci a yankin na Sahel na nuni da cewa dole ana bukatar karin kudin don yakin da 'yan ta'addan.
A cewar EU tsanantar ayyukan ta'addanci a yankin na Sahel na nuni da cewa dole ana bukatar karin kudin don yakin da 'yan ta'addan. REUTERS/Michel Euler/Pool
Talla

Yayin wani taro da yanzu haka ke ci gaba da gudana a kasar Mauritania guda cikin kasashen yankin na Sahel da ke fuskantar barazanar ta’addanci, shugaban sashen raya kasashe na kungiyar EU Neven Mimica ya ce yanzu haka sun hada kudin da ya tasamma yuro biliyan 800 ciki har da wanda suka samu tallafinsa a yau Alhamis.

A cewar ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian kasar za ta karo yuro miliyan 220 akan wanda ta bayar da farko yuro miliyan 280 don fatattakar ayyukan ta’addancin da kuma sake gina kasashen yankin na Sahel.

Kasashen yankin na Sahel da suka kunshi Mauritania Burkinafaso Chadi Mali da kuma Jamhuriyar Nijar sun nuna bukatar samun tallafin akalla yuro biliyan 1 da miliyan dari 9 don kammala ayyukan da suka sanya a gaba wajen yakar ‘yan ta’adda da kuma daidaita tsaro baya ga bunkasa ci gabansu.

Sai dai a cewar Ministan harkokin wajen na Faransa, kasar ba za ta iya bayar da cikon yuro miliyan 220 da ta alkawarta ba har sai zuwa nan da shekaru biyu.

Cikin ayyukan da za a gudanar da kudaden a cewar kasashen 5, sun kunshi gina makarantu, asibitoci samar da ruwan sha da ma hanyoyin sufuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.