Isa ga babban shafi
Wasanni

CAF ta haramtawa Saliyo shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika

Hukumar kula da kwallon kafar Afrika CAF, ta haramtawa kasar Saliyo shiga gasar cin kofin nahiyar ta shekarar 2019, bayan soke sunan kasar daga cikin wasannin neman cancantar halartar gasar.

Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na kasar Saliyo.
Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na kasar Saliyo. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Matakin CAF ya zo ne bayan hukuncin da hukumar kwallo ta duuniya FIFA ta yanke na dakatar da ita daga wasanni a watan Oktoba, saboda katsalandan din da gwamnatin kasar ta yi a harkokin hukumar wasannin kasar ta Saliyo.

Matakin haramcin kan Saliyo, ya baiwa kasashen Kenya da Ghana dake rukuni na 6 a jadawalin wasannin neman cancantar zuwa gasar kofin nahiyar Afrika damar samun guraben matsayi na farko da na biyu.

Lamarin ya samu asali ne bayan da hukumar yakar cin hanci da Rashawa ta Saliyon ta kori shugabar hukumar kwallon kasar Isha Johansen da sakatarenta Christopher Kamar saboda samunsu da laifukan almundahana da Sibaran na bayyen yashe kudaden hukumar.

Hakan ce ta sa tun a watan Oktoba CAF ta soke wasanni guda biyu na neman cancantar halartar gasar cin kofin nahiyar Afrika da kasar ta Saliyo za ta buga da Ghana, saboda takkadamar dake tsakanin gwamnatin kasar da FIFA.

A karshen makon da ya kare ne dai CAF ta karbe damar da ta baiwa kasar Kamaru ta karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika da za’a yi a shekarar 2019 mai kamawa, saboda rashin kyakkyawan shirin kasar dangane da gasar.

Kawo yanzu dai CAF bata tantance kasar da za ta karbi bakuncin gasar ba, sai dai Afrika ta Kudu ta tabbatar da cewa, hukumar ta CAF ta yi mata tayin bata damar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.