Isa ga babban shafi
Duniya

Yan jaridu kusan 30 ne suka rasa rayukan su a Duniya cikin shekaru 2

Sabbin alkaluma da kungiyar Reporters Sans Frontieres ta fitar na nuni da cewa an kashe akalla ‘yan jaridu 30 lokacin da suke kan ayyukansu cikin shekaru biyu da suka gabata a sassan Duniya. 

Tambarin kungiyar kare yan jaridu ta Reporters Sans Frontieres
Tambarin kungiyar kare yan jaridu ta Reporters Sans Frontieres rsf.org
Talla

Kungiyar ta ce ‘yan jaridu da ke bincike kan batutuwa masu sarkakkiya ne suka fi haduwa da ajalinsu, musamman a kasashen China, Rasha, Colombia, Malta da kuma Slovakia.

A watan Agusta Kungiyar ta ce akalla 'yan Jaridu 63 aka kashe bana, tare da wasu masu ba da bayanai 11 da masu taimakawa 'Yan Jaridu 4, kuma cikin wadanda aka kashe har da Dan Jaridar Saudiyya, Jamal Khashoggi.

Wannan adadi ya zarce na shekarar bara wanda ya nuna cewar Yan Jaridu 55 aka kashe.

Cikin wadanda suka taba lashe kyautar kungiyar sun hada da Liu Xiabo daga China da Raif Badawi daga saudiyya da Jaridar Cumhuriyat daga Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.