Isa ga babban shafi
CAF

Hukumar CAF na taro dangane da gasar Afirka a Kamaru a 2019

A yau juma’a ne hukumar kwallon kafar Afirka CAF zata gudanar da taron ta da zai mayar da hankali zuwa ga shirya gasar cin kofin Afirka a Kamaru na shekara ta 2019, taron na Accra a kasar Ghana, yanzu haka daya daga cikin kwamitin da aka dorawa nauyin gudanar da bincike ya mayar da hankali zuwa batutunwan da suka shafi tsaro, yayinda kwamitin na biyu ya duba bangaren gine-ginen filayen wasanni.

Tambarin hukumar kwallon kafar Afrika na CAF
Tambarin hukumar kwallon kafar Afrika na CAF Courtesy of CAF
Talla

Jan kaffa da ake fuskanta a kai kamar dai yadda bincike ya tabbatar zai iya tilastawa zaman na yau canza kasa da zata karbi bakuncin wadanan wasanni, akasin haka dage gasar zuwa shekara ta 2021 ko 2023 a Kamaru.

A daya geffen kasancewar manema labarai da dama na Kamaru a Accra dake bayyana cewa kasar su ta gudanar da manyan ayuka tareda da kamala gina wasu filayen wasanni, haka zalika Shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya daga cikin manyan alkawura da ya dau a lokacin yakin zabe na watan Oktoba shine na karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika na shekara ta 2019.

Dage wannan gangami kan iya janyo fushin da dama daga cikin yan Kamaru.

Da jimawa yan kamaru na kallon Shugaban hukumar CAF Ahmad Ahmad a matsayin wanda ke kokarin hana ruwa gudu tun bayan da ya canji Issa Hayatou daga kujerar Shugabancin hukumar kwallon kafar Afrika.

Yayinda suka rage watanni bakwai a gudanar da gasar cin kofin Afrika, dage wasanni nada matukar wahala a cewa masana, ko kuma canza kasa zuwa wata kasa kamar Cote D’Ivoire ko Guinee wanda da za su karbi gasar cin kofin Afrika na shekara ta 2021 da 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.