Isa ga babban shafi
Afrika-Tafkin Tchadi

Shugabannin yankin tafkin Chadi na taro kan Boko Haram

Shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi na gudanar da wani taro a yau Alhamis a birnin Njamena na kasar Chadi domin tattaunawa kan zafafan hare-haren baya-bayan nan da kungiyar Boko haram ta kaddamar a yankin wanda ya haddasa rasa rayukan tarin dakarun soji baya ga fararen hula.

Rundunar hadakar yaki da Boko Haram ta kasashen yankin tafkin tchadi
Rundunar hadakar yaki da Boko Haram ta kasashen yankin tafkin tchadi twetter
Talla

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Nijar Mahamadou Issofou suka isa birnin na Njamena yayinda suka gana da Shugaba Idris Deby na chadi.

Dakarun wadannan kasashe da kuma na Kamaru na hada kai wajen yaki da mayakan boko haram a yankin tafkin Chadi a karkashin rundunar hadin gwuiwa.

Ganawar shugabannin uku na zuwa ne bayan ziyarar gani da ido da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai sansanin sojin kasar da ke Matele a jihar Bornon, wurin da boko haram ta hallaka tarin dakarun kasar.

A jawabansa, Muhammadu Buhari ya ce dole ne aga bayan kungiyar ta Boko Haram tare da kawo karshen ta'addancin kungiyar a yankin Tafkin Chadi.

Wani rahoto na nuni da cewa sama da mutane dubu 27 suka rasa rayukansu tun fara rikicin Boko Haram, wanda ya fi tsananta a yankin arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2009.

Haka zalika mutane akalla miliyan 1 da dubu dari 8 suka rasa matsuguninsu, sakamakon rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.