Isa ga babban shafi
Wasanni-Najeriya

Super Falcons ta Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 4 da 2

Tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya bangaren mata Super Falcons ta yi nasarar zuwa wasan karshe na cin kofin Afrika bayan doke takwararta ta Kamaru da ci 4 da 2 a wasan da aka kammala dazu dazun nan.

Super Falcons wadda ta dage kofin Afrika har sau 8 a tarihi yanzu haka ita ce kasar Afrika da za ta halarci gasar cin kofin duniya da Faransa za ta karbi bakonci a bana.
Super Falcons wadda ta dage kofin Afrika har sau 8 a tarihi yanzu haka ita ce kasar Afrika da za ta halarci gasar cin kofin duniya da Faransa za ta karbi bakonci a bana.
Talla

Gasar wadda ke ci gaba da gudana a Ghana yanzu haka, sai da aka shafe tsawon mintuna 120 ana fafatawar tsakanin kungiyoyin biyu ba tare da nasarar zura kwallo ba, dalili kenan da ya sanya aka koma bugun daga kai sai mai tsaron raga inda Super Falcons ta yi nasarar zura kwallayenta hudu ta kuma barar da biyu daga Kamaru.

Nasarar ta Super Falcons wadda kawo yanzu ta ke rike da kambun na kofin Afrika har guda 8 kai tsaye ya bata tikitin samun gurbi a gasar cin kofin duniya bangaren mata da Faransa za ta karbi bakonci a bana.

Kafin nasarori na baya-bayan nan Najeriyar ta faro wasan na gasar cin nkofin Afrika bangaren mata da kafar hagu, inda Afrika ta kudu ta samu nasara kanta da kwallo 1-0, amma daga bisani a sauran wasanninta na rukuni, Najeriya ta lallasa Zambia da kwallye 4-0, haka zalika Equatorial Guinea da kwallaye 6-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.