Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Moussa Aksar kan bayanan da ke nuna tsaurin aikin Jarida a Jamhuriyar Nijar

Wallafawa ranar:

Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen da ake da dimbin kafafen yada labarai masu zaman kansu, to sai dai ana bayyana aikin jarida da cewa yana da matukar wuya a kasar.Moussa Aksar, mamallakin jaridar Evenement, daya daga cikin jaridun da ake bugawa a kasar, ya shahara sakamakon wallafa wasu bayanai da ke da matukar sarkakkiya, inda a shekarun baya ya taba kayar da tsohon shugaban Libya marigayi Mu’ammar Kaddafi a gaban kotu, kafin daga bisani ya wallafa wani labari dangane da cinikin jarirai wanda ya yi awon gaba da ‘yan siyasa da dama, tare da tilasta wa wasu yin hijira domin barin kasar. Na zatan da Moussa Aksar dangane da wadannan batutuwa, ga kuma zantawarmu.

Fitaccen dan Jarida a Jamhuriyar Nijar Moussa Aksar.
Fitaccen dan Jarida a Jamhuriyar Nijar Moussa Aksar. Reuters
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.