Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Hussainin Manguno kan zargin da Eeben Barlow ya yi na cewa Buhari ya siyasantar da yaki da Boko Haram

Wallafawa ranar:

WANI kwamandan sojin hayar Afirka ta kudu da gwamnatin Najeriya ta taba hayar su domin yaki da kungiyar boko haram Eeben Barlow, ya zargi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da siyasantar da lamarin tsaro, abinda ke haifar da matsala yanzu haka.Gwamnatin Goodluck Jonathan ce ta yi hayar kamfanin tsaron STTEP daga Afirka ta kudu a shekarar 2015 domin taimakawa sojin Najeriya yaki da boko haram, amma sai gwamnatin Buhari ta soke kwangilar.Barlow ya ce kamfanin na sa da ya yi suna wajen horar da soji da kuma kariya ya taimaka wajen kwato yankunan da ke hannun book haram kafin zuwan gwamnatin Buhari, inda ya ke cewa sun san za’a samu hare haren da Najeriya ke samu yanzu haka.Akan wannan batu ne Ahmad Abba ya tattauna da masanin harkar tsaro, Hussainin Manguno kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Kwamandan sojin wanda kamfaninsa ya yi kaurin suna wajen yaki a kasashe daban-daban ya ce idan da Buhari bai soke kwangilar da suka faro ba da tuni yaki da boko haram ya zama tarihi.
Kwamandan sojin wanda kamfaninsa ya yi kaurin suna wajen yaki a kasashe daban-daban ya ce idan da Buhari bai soke kwangilar da suka faro ba da tuni yaki da boko haram ya zama tarihi. RFI/OR
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.