Iyalan Sophie Petronin na kira zuwa Shugaba Macron
Tsawon shekaru biyu babu duri’ar yar kasar Faransa nan Sophie Petronin da wasu yan bindiga suka yi awon gaba da ita a Gao dake kasar Mali.A jiya asabar daya daga cikin ya‘an ta Sebastien Chadaud Petronin a wata zantawa da manema labarai na Afp,Rfi da Radio Faransa ya bukaci Shugaban Faransa ya kara basu karin haske da kuma sanar da matsayar sa dangane da abinda hukumomin Faransa ke yi a kai.
Wallafawa ranar:
Sebastien Chadaud Petronin da ya samu isa kasar Mauritania ya karasa da cewa kasancewar sa Afrika , ita ce ta neman shiga tattaunawa da masu garkuwa da mahaifiyar sa.
Idan aka yi tuni ranar 24 ga watan Disemba na shekara ta 2016 a birnin Gao wasu yan bindinga suka yi awon gaba da wannan mata mai shekaru 73.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu