Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan tarin dakarunta a Matele

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da rahotanni da ke nuna cewar mayakan boko haram sun kai kazamin hari kan sansanin sojin runduna ta 157 da ke Matele a karamar hukumar Guzamala ta Jihar Barno, tare da hallaka tarin sojoji.

Babban Hafson Sojin Najeriya Lieutanan Janar Tukur Yusuf Buratai.
Babban Hafson Sojin Najeriya Lieutanan Janar Tukur Yusuf Buratai. thenewsnigeria
Talla

Wata sanarwar da rundunar ta rabawa manema labarai, ta kare matakin da ta dauka na kin sanar da harin da wuri domin bin ka’idodin ayyukan ta na tattara bayanai da kuma shaidawa ‘yan uwan sojin da harin ya ritsa da su.

Rundunar ta gargadi masu yada jita jita da hotunan harin da kuma kafofin yada labarai da su dinga tuntubar ta domin samun sahihan bayanai maimakon yada jita jitar da zai karfafa Yan ta’adda.

Tuni dai harin ya haifar da mahawara a kafofin sada zumunta tare da bai wa 'yan siyasa damar tafka mahawara akai da kuma neman ganin gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya cikakken bayani akai.

Rahotanni sun ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira taron manyan hafsoshin sojin kasar domin duba matsalar, yayin da ya tura ministan tsaro Mansur Dan Ali Chadi domin tattaunawa da hukumomin kasar.

Majalisar Dattawan Najeriya ta dage zaman ta a makon nan domin nuna juyayi kan kazamin harin, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fitar da sanarwa yana bayyana alhinin sa da harin.

Bayanai sun ce an kashe sojojin Najeriya sama da 40, amma ya zuwa yanzu rundunar sojin bata bada adadin wadanda suka mutu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.