Isa ga babban shafi
Afrika-IS

IS ta yi ikirarin kisan mutane 118 a yammacin Afrika cikin mako 1

Kungiyar IS ta yi ikirarin kisan akalla mutane 118 cikin mako guda a kasashen yammacin Afrika da suka hadar da Najeriya da Nijar da Jamhuriyar Chadi sanadiyyar jerin hare-haren da ta kaddamar a kasashen 3.

Abubakar Shekau.
Abubakar Shekau. AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Ikirarin na IS na zuwa ne bayan wasu jerin hare-hare da boko haram ta kai kan sansanin sojin Najeriya da ya hallaka fiye da 70 baya ga raunata daruruwa cikin makon nan matakin da ke ci gaba da sanya tsoro a zukatan fararen hula.

Cikin wani sako da kungiyar ta IS ta saki a wani faifan bidiyo, ta ce daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Nuwamba ta kaddamar da hare-hare 5 da suka hallaka mutanen su 118 a Najeriya da Chadi.

Harin kan sansanin sojin na Najeriya shi ne mafi muni da aka taba kai wa wanda ta ke ya hallaka mutane 44 ko da dai wani ganau a lokacin da ake fitar da gawarwakin a garin Matete da ke kan iyakar Najeriyar da Nijar, ya ce an fitar da gawa ta fi ta mutum 100.

Wannan dai ne karo na bakwai da Boko Haram ko kuma IS ke yunkurin kai makamancin harin kan sansanin ko da dai dakarun sojin na dakilewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.